Kotu Ta Bada Umarnin kwace littatafan Abduljabar Kabara Da kuma bayar da umarnin rushe masallatansa. ko da yake har yanzu kotun bata bayyana ranar da za a rataye fitaccen malamin ba. Kotu a jihar Kano da ke Najeriya, ta yankewa fitaccen malamin nan Abduljabbar Nasiru Kabara hukuncin kisa ta hanyar rataya, bayan samunsa da laifin tayar da zaune tsaye da kuma bata suna ga fiyayyen halitta (S.A.W) Daga nan kuma ya yanke wa wanda ake tuhuma hukunci kan tuhume-tuhumen da ake yi masa. An dai gurfanar da Kabara a gaban kotu kan lamarin da ya shafi kalaman batanci ga Manzon Allah (SAW), matakin da ke iya tada zaune tsaye. A watan Yulin 2021 ne gwamnatin jihar Kano ta gurfanar da shi. Abduljabbar dai ya bayyana gaban kotun cikin nutsuwar da ba’a taba gani ba tun bayan fara shari’ar, yana mai ban carbi tare da sauraron karar. Da aka tambaye shi ko yana da wani abu da zai fada wa kotun, Barista Aminu Ado Abubakar, wanda ya tsaya a matsayin lauyan wanda ake kara, ya roki kotun da ta yi wa wan...
Hotunan Yadda Jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna ya taka wata mota a Kubwa da ke birnin Abuja, Wanda Yayi Sanadiyar mutum daya ya rasa ransa.
Hotunan Yadda Jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna ya taka wata mota a Kubwa da ke birnin Abuja, Wanda Yayi Sanadiyar mutum daya ya rasa ransa.