Rundunar 'yan sandan Jihar Nasarawa a arewacin Najeriya ta ce ta kama wani dattijo mai shekara 75 kan zargin yi wa 'yar ɗan uwansa fyaɗe mai shekara huɗu.
Sanarwar da kakakin 'yan sanda DSP Ramhan Nansel ya fitar a yau Lahadi ta ce sun kama Isa Nana Okpoku ne bayan wani rahoto da aka kai hedikwatar rundunar ranar Asabar.
Binciken farko-farko da rundunar ta gudanar ya nuna cewa dattijon na zaune da yarinyar a gida ɗaya da ke Daddare a yankin Ƙaramar Hukumar Obi.
"Isa Nana ya yaudari ƙaramar yarinyar zuwa ɗakinsa kuma ya yi lalata da ita," a cewar sanarwar. "An garzaya da ita asibiti don yin gwaji, inda likita ya tabbatar da cewa lamarin ya faru."
Sanarwar ta ƙara da cewa Kwamashinan 'Yan Sanda Maiyaki Mohammed Baba ya ba da umarnin gudanar da cikakken bincike da kuma ɗaukar matakin shari'a a kan wanda ake zargi da zarar an kamamala.
Comments
Post a Comment