Skip to main content

Za Mu Tabbatar An Gudanar Da Ingantaccen Zabe A 2023 – Sojoji

 Babban Hafsan Sojojin Kasa na Najeriya, Laftanar-Janar Faruk Yahaya, ya ce sun shirya tsaf domin tabbatar da an gudanar da ingataccen zabe a shekarar 2023 mai zuwa.


Ya ba da tabbacin ne lokacin da yake jawabi a bikin yaye kuratan sojojin kasa da aka yi a makarantar kurata da ke Zariya, a jihar Kaduna ranar Asabar.


Aminiya ta rawaito cewa sabbin kurata 6,226 ne aka yaye daga makarantar horas da sojojin da ke Zariya.

Babban Hafsan ya bukaci sabbin kuratan da su kasance masu biyayya ga tsarin aiki da ladabi da kuma bin na gaba wurin tafiyar da muhimman manufofin rundunar sojin.

Faruk Yahaya, ya ce a daidai lokacin da Najeriya ke fama da matsalolin tsaro, rundunar za ta ci gaba da iya bakin kokarinta don ganin sun kawar da sauran kalubalen da ke gabansu da kuma tabbatar da doka da oda a sassan iasar nan.

Daga nan sai ya yaba da kokarin da sarakuna iyayen jasa ke yi don cigaban ɓangaren tsaro da samar da zaman lafiya.




Comments

Popular posts from this blog

Kotu Ta Bada Umarnin kwace littatafan Abduljabar Kabara Da kuma bayar da umarnin rushe masallatansa

 Kotu Ta Bada Umarnin kwace littatafan Abduljabar Kabara Da kuma bayar da umarnin rushe masallatansa. ko da yake har yanzu kotun bata bayyana ranar da za a rataye fitaccen malamin ba. Kotu a jihar Kano da ke Najeriya, ta yankewa fitaccen malamin nan Abduljabbar Nasiru Kabara hukuncin kisa ta hanyar rataya, bayan samunsa da laifin tayar da zaune tsaye da kuma bata suna ga fiyayyen halitta (S.A.W) Daga nan kuma ya yanke wa wanda ake tuhuma hukunci kan tuhume-tuhumen da ake yi masa. An dai gurfanar da Kabara a gaban kotu kan lamarin da ya shafi kalaman batanci ga Manzon Allah (SAW), matakin da ke iya tada zaune tsaye. A watan Yulin 2021 ne gwamnatin jihar Kano ta gurfanar da shi. Abduljabbar dai ya bayyana gaban kotun cikin nutsuwar da ba’a taba gani ba tun bayan fara shari’ar, yana mai ban carbi tare da sauraron karar. Da aka tambaye shi ko yana da wani abu da zai fada wa kotun, Barista Aminu Ado Abubakar, wanda ya tsaya a matsayin lauyan wanda ake kara, ya roki kotun da ta yi wa wan...

Peter Obi Bazai Iya Lashe Zaben 2023 ba___Chewar Gwamnan Jihar Anambra

 Peter Obi ba zai iya lashe zaɓen 2023 ba, Cewar Gwamnan Anambra Soludo. Gwamnan jihar Anambra Chukwuma Soludo, ya bayyana cewa jam’iyyar Labour (LP) na Peter Obi ba za ta lashe zaben 2023 ba.”  Soludo ya bayyana hakan ne a ranar Litinin a wata kasida mai suna ‘Tarihi ya nuna kuma ba zan yi shiru ba (Sashe na 1).  Ya ce: “Bari ya bayyana sarai: Peter Obi ya san cewa ba zai iya ba kuma ba zai yi nasara ba. Ya san wasan da yake yi, shi ma ya sani, kuma ya san na sani.   “Wasan da yake bugawa shine  babban dalilin da yasa bai koma APGA ba. Gaskiyar mugunyar gaskiya (wasu kuma za su ce, Allah Ya kiyaye) ita ce, akwai mutane biyu jam'iyun da ke neman takarar shugaban ƙasa, Jam'iyyun sune kamaraka APC da PDP sauran wasan kwaikwayo ne mai ban sha'awa.” Gwamanan ya ƙara da cewa ya riga da ya faɗa masa ra’ayinsa, Lallai babu wata tafarki ingantacciya gare shi a kusa da mukamai biyu na farko, kuma idan ba a kula ba, ba zai ma kusanci matsayi na uku ba ko da a wurin ƙ...

Cikin Hotuna

Hotuna: Comrd Bashir Yau Bashowa Hotunan Yadda: Maigirma Gwamnan Jihar Katsina Alh Aminu Bello Masari, ya Jagoranchi taron masu ruwa da tsaki na Jam'iyyar APC, wanda  ya gudana yau Lahadi a dakin taro na gidan Gwamnati.