YANZU-YANZU: Hukumar 'yan sanda ta yi nasarar cafke mutumin da yake bawa 'yan Bindiga Asiri tare da rigan layu a Katsina
Rundunar yan sandan jihar Katsina, ta yi nasarar cafke kasurgumin boka, Sani Bello dan shekara 53 da haihuwa da ya ke zaune akan titin Maiduguri a karamar hukumar Sabuwa ta jihar Katsina, da ya shahara wajen baiwa yan bindiga Sa'a da kuma yi masu rigar layu, wadda ko an harbe su da bindigar ba ta samun su.
Kakakin rundunar yan sandan jihar Katsina, SP Gambo Isa ya bayyana manema labarai cewa a cikin binciken da ake yi masa, an samu rigar layu guda huɗu mallakinsa kuma yana saida duk guda akan Kuɗi Naira dubu sittin.
Comments
Post a Comment