Kotu Ta Bada Umarnin kwace littatafan Abduljabar Kabara Da kuma bayar da umarnin rushe masallatansa.
ko da yake har yanzu kotun bata bayyana ranar da za a rataye fitaccen malamin ba.
Kotu a jihar Kano da ke Najeriya, ta yankewa fitaccen malamin nan Abduljabbar Nasiru Kabara hukuncin kisa ta hanyar rataya, bayan samunsa da laifin tayar da zaune tsaye da kuma bata suna ga fiyayyen halitta (S.A.W)
Daga nan kuma ya yanke wa wanda ake tuhuma hukunci kan tuhume-tuhumen da ake yi masa.
An dai gurfanar da Kabara a gaban kotu kan lamarin da ya shafi kalaman batanci ga Manzon Allah (SAW), matakin da ke iya tada zaune tsaye. A watan Yulin 2021 ne gwamnatin jihar Kano ta gurfanar da shi.
Abduljabbar dai ya bayyana gaban kotun cikin nutsuwar da ba’a taba gani ba tun bayan fara shari’ar, yana mai ban carbi tare da sauraron karar.
Da aka tambaye shi ko yana da wani abu da zai fada wa kotun, Barista Aminu Ado Abubakar, wanda ya tsaya a matsayin lauyan wanda ake kara, ya roki kotun da ta yi wa wanda ake tuhuma sassauci domin ya aikata abin da ya aikata bisa rashin sani
Sai dai Abduljabbar ya mike yana fadin bai san lauyan ba, kuma shine karon farko da ya fara ganinsa.
“Ban san shi ba. Wannan shine karo na farko da nake ganinsa. Kada a bar shi ya yi magana a madadina. Zan iya kuma ya kamata a bar ni in yi magana da kaina,” in ji Abduljabbar.
Comments
Post a Comment