WAYAYYAR MACE.
-
❝Wayayyiyar mace itace macen da ta iya tarairayar mijinta a lokacin da yake cikin halin ƙuncin rayuwa ko wata fargaba, ba wacce za ta sake cusa masa wani baƙin cikin akan baƙin cikin da ya shigo dashi cikin gida ba. Da yawan matan da suka yi wayewar addini, ko kuma suka san martabar aurensu, da zarar sunga ran mazajensu su ya ɓaci, to sun san salon da za subi domin su kwantar musu da hankali, su yaye musu wannan baƙin cikin da suka shigo dashi cikin gida❞
-
"Ba wai sai lallai ilmin addini ko na rayuwa bane kaɗai yake zamtowa wayewa, ki san yadda za ki farantawa mai gidanki rai a lokacin da ransa ya ɓaci wannan ma wayewa ce ta musamman"
-
"Da yawan wasu ma'auratan basu san yadda za su gusarwa da junansu wani baƙin cikin da yake damun ɗayan sashensu ba, za ka samu wata matar bata iya sanyayawa mijinta rai ba a lokacin da taga ransa a ɓace, haka nan za ka sami wani mijin bai iy sanyayawa ran matarsa ba a lokacin da yaga ranta a ɓace, wanda kuma hakan yakan iya kawo naƙasu da rashin jin daɗin zamantakewar aure a tsakaninsu"
-
Allah ta'ala yasa mu dace baki ɗaya.
Comments
Post a Comment