Taƙaitaccen Tarihin Shahararren Malamin addini Sheikh Abubakar Mahmud Gumi.
Daga Janaidu Amadu Doro.
“An haifi Sheikh Abubakar Mahmud Gumi a garin Gumi da ke jihar Sokoto Kafin daga bisani ta zama cikin jihar Zamfara a shekara ta 1340 bayan Hijira daidai da shekarar Miladiyya ta 1922.
Sheikh Gummi ya tashi ne cikin kyakkyawar tarbiyya da natsuwa da tsafta da neman Ilimi ƙarƙashin kulawar mahaifinsa Kuma shi ne Alkalin Gummi na wancan lokacin.
Tarihi ya Ambato cewar Marigayi Sheik Gumi ya yi karance-karance na zaure a wurare daban-daban na Malaman da su ka shahara a ƙasar Hausa a wancan lokaci tare da karatu na Nizamiyya har kasar Sudan da kasar Saudiyya.
Shehin malamin ya na ɗaya daga cikin shahararrun malaman Addinin Musulunci a Afrika baki ɗaya.”
“Sheikh Gummi mutum ne Mai kokarin binciken Al'kur'ani da Sunna kan hukunce-hukuncen Shari’a tun daga abinda ya shafi Tauhidi, Hadisi, Fikhu da luggar Larabci.
Ya yi rubuce-rubuce masu yawa kuma kadan daga cikinsu sun hada da:
Al-akeedatus Saheehah bi Muwaafakatish Shari’ah.
Tarjamar Ma’a’nonin Al-kur’ani Mai Girma.
“Tafsirin Al-kur’ani. Raddul Azhaan ilaa Ma’aanil Kur’an.
Tarjamar littafin Hadisin “Arba’uunan Nawawiy”.
Littafi mai suna "Manufata".
Sheik Abubakar Mahmud Gumi ya rasu a ranar 11 ga watan Satumbar shekarar 1992.
Allah ya jikansa da Rahama ya sa kwanciya hutu ce.
Comments
Post a Comment