Gwamnati Zata Raba Naira Biliyan 2.6 Ga Waɗanda Rikicin 'Yan Bindiga Ya Shafa A Jihar Katsina
Gwamnatin jihar Katsina ta amince da biyan Naira biliyan 2,671,330,300 ga mutane 13,315 da rikicin 'yan bindiga ya rutsa da su a faɗin Jihar Katsina
Amincewar ta biyo bayan da kwamitin da Gwamnatin ta kafa don zaƙulo da tantance mutanen tun daga shekarar 2020 ya gabatar da rahoton shi.
Mai baiwa gwamna Aminu Bello Masari shawara na musamman kan ilimi mai zurfi Bashir Usman Ruwan Godiya, wanda ya bayyana wa manema labarai sakamakon taron majalisar zartarwa na jiha karo na biyar.
Ya ce za'a yi amfani da kuɗaɗen ne wajen samar da kayan abinci da kayan makaranta da kayan sawa da kuma ilimi da kuma biyan wasu buƙatu na mata da marayu da aka kashe iyayen su.
Ya ce tuni gwamnati ta sake kafa wani kwamiti domin aiwatar da shawarwarin
Comments
Post a Comment