Skip to main content

Gobna Matawale Jihar Zamfara Ya Gargadi Hukumar EFCC Bisa Zargin Bata Mashi Suna

 Gwamnan Jihar Zamfara Bello Matawalle, Ya Kalubalanci Tare Da Gargardin Hukumar EFCC Kan Yunkurin Bata Masa Suna


Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle, ya bawa EFCC dama akan su shiga duk inda sukeso domin binciken duk abunda suke son bincike akansa da Gwamnatinsa, da duk inda yake da kaddara a duniya. 


Gwamnan ya kalubalanci EFCC akan wani labarin kage da karya wanda jaridar karya da sharri ta Sahara Reporters ta watsa cewa anboye wasu makudan kudade awasu wurare domin biyan ma'aikatan gwamnatin Zamfara albashi ta tsarin "Table Payment" wanda daga shugaban Hukumar EFCC kalaman suka fito.


Gwamna Matawalle ta hanyar babban Lauyansa Mike Azkhome SAN, ya rubutu dogowar takarda ga shugaban Hukumar EFCC, akan yana gargardinsu da su kare kansu kuma su bincike duk inda kaddarar shi take da kuma duk inda suke tunanin anboye kudaden al-umma, haka zalika Gwamnan ya gargardi hukumar EFCC akan su daina yunkurin bata masa suna ko ko kuma bayarda kafa ga 'yan adawar siyasar sa akan cimma wata manufa tasu ta siyasa akan kazafi, karya da kage gareshi da Gwamnatinsa. 


Gwamna Bello Matawalle, yace duk lokacinda suka tashi binciken nasu zai hadasu da mutane aminansa guda ukku domin su saka ido akan yanda EFCC zasuyi aikinsu domin kaucewa yaudara da kuma zamba cikin Aminci. 


Gwamna Bello Matawalle yace ya zama dole EFCC su aiwatarda binciken ko kuma yanemi hakkinsa gaban kuliya akan kokarin bata masa suna a idon duniya amatsayinsa na dan Adam dan kasa mai cikkaken hakki. Haka kuma dolene ya barrantarda Gwamnatinshi wajen maka hukumar EFCC kotu domin neman hakki. 


Gwamnan yace yayi mamaki matuka akan irin yanda hukumar EFCC ke Furta kalamai ba tare da tabbatarda gaskiyar lamari ba wanda hakan zai kawo shakku ga ingancin hukumar EFCC ga Al-umma. 


Gwamna Matawalle, yace yana jira yaga dukkannin matakin da hukumar EFCC zata dauka akan kodai su fito su bayyana yadda lamarin yake akan gaskiya ko kuma ya garzaya dasu kotu domin neman hakkinsa.





Comments

Popular posts from this blog

Kotu Ta Bada Umarnin kwace littatafan Abduljabar Kabara Da kuma bayar da umarnin rushe masallatansa

 Kotu Ta Bada Umarnin kwace littatafan Abduljabar Kabara Da kuma bayar da umarnin rushe masallatansa. ko da yake har yanzu kotun bata bayyana ranar da za a rataye fitaccen malamin ba. Kotu a jihar Kano da ke Najeriya, ta yankewa fitaccen malamin nan Abduljabbar Nasiru Kabara hukuncin kisa ta hanyar rataya, bayan samunsa da laifin tayar da zaune tsaye da kuma bata suna ga fiyayyen halitta (S.A.W) Daga nan kuma ya yanke wa wanda ake tuhuma hukunci kan tuhume-tuhumen da ake yi masa. An dai gurfanar da Kabara a gaban kotu kan lamarin da ya shafi kalaman batanci ga Manzon Allah (SAW), matakin da ke iya tada zaune tsaye. A watan Yulin 2021 ne gwamnatin jihar Kano ta gurfanar da shi. Abduljabbar dai ya bayyana gaban kotun cikin nutsuwar da ba’a taba gani ba tun bayan fara shari’ar, yana mai ban carbi tare da sauraron karar. Da aka tambaye shi ko yana da wani abu da zai fada wa kotun, Barista Aminu Ado Abubakar, wanda ya tsaya a matsayin lauyan wanda ake kara, ya roki kotun da ta yi wa wan...

Peter Obi Bazai Iya Lashe Zaben 2023 ba___Chewar Gwamnan Jihar Anambra

 Peter Obi ba zai iya lashe zaɓen 2023 ba, Cewar Gwamnan Anambra Soludo. Gwamnan jihar Anambra Chukwuma Soludo, ya bayyana cewa jam’iyyar Labour (LP) na Peter Obi ba za ta lashe zaben 2023 ba.”  Soludo ya bayyana hakan ne a ranar Litinin a wata kasida mai suna ‘Tarihi ya nuna kuma ba zan yi shiru ba (Sashe na 1).  Ya ce: “Bari ya bayyana sarai: Peter Obi ya san cewa ba zai iya ba kuma ba zai yi nasara ba. Ya san wasan da yake yi, shi ma ya sani, kuma ya san na sani.   “Wasan da yake bugawa shine  babban dalilin da yasa bai koma APGA ba. Gaskiyar mugunyar gaskiya (wasu kuma za su ce, Allah Ya kiyaye) ita ce, akwai mutane biyu jam'iyun da ke neman takarar shugaban ƙasa, Jam'iyyun sune kamaraka APC da PDP sauran wasan kwaikwayo ne mai ban sha'awa.” Gwamanan ya ƙara da cewa ya riga da ya faɗa masa ra’ayinsa, Lallai babu wata tafarki ingantacciya gare shi a kusa da mukamai biyu na farko, kuma idan ba a kula ba, ba zai ma kusanci matsayi na uku ba ko da a wurin ƙ...

Cikin Hotuna

Hotuna: Comrd Bashir Yau Bashowa Hotunan Yadda: Maigirma Gwamnan Jihar Katsina Alh Aminu Bello Masari, ya Jagoranchi taron masu ruwa da tsaki na Jam'iyyar APC, wanda  ya gudana yau Lahadi a dakin taro na gidan Gwamnati.