Skip to main content

Sufeto Janar Ya Dora Laifin Rikicin Suyasa Akan Gwamnoni

 2023: Sifeto-Janar ya ɗora laifin rikicin siyasa a kan gwamnoni


Sufeto-Janar na ƴan sanda, Usman Baba, ya ɗora laifin karuwar tashe-tashen hankulan siyasa a kasar kan wasu gwamnonin jihohi.


 Baba ya bayyana haka ne a wata ganawa da ya yi da shugabannin jam’iyyun siyasa da sauran masu ruwa da tsaki a yau Alhamis a Abuja.


Ya ce an kira taron ne domin jan hankalin shugabannin jam’iyyun siyasa kan yadda ake samun karuwar tashe-tashen hankula a siyasance da kuma gabatar da cikakken tsari na magance matsalolin.


“Muna ta samun rahotannin wasu Gwamnonin Jihohi da ke karfafa ‘yan barandan siyasa.


“Suna amfani da jami'an tsaro na kananan hukumomin da ke karkashinsu domin tada tarzoma a wajen yakin neman zabe na jam’iyyu da aka bada umarni, musamman sabanin ra’ayi na siyasa.


“A yin haka, suna amfani da ikonsu da tasirinsu don hana kafa allunan yakin neman zabe ko kuma su kakkarya su.


"Suna kuma hana ƴan adawar siyasa filaye su gudanar da yakin neman zabensu ko kuma yin taron su na siyasa cikin lumana, wanda hakan ya saɓa wa tanadin dokar zabe ta 2022 (Kamar yadda aka gyara)," in ji shi.


IGP ya ce ya kuma ɗora alhakin mafi yawan tashe-tashen hankula a kan tsattsauran ra'ayi na siyasa, rashin fahimtar juna, rashin hakuri, kuskuren siyasa, kalaman kiyayya, da kuma tunzura jama'a.





Comments

Popular posts from this blog

Kotu Ta Bada Umarnin kwace littatafan Abduljabar Kabara Da kuma bayar da umarnin rushe masallatansa

 Kotu Ta Bada Umarnin kwace littatafan Abduljabar Kabara Da kuma bayar da umarnin rushe masallatansa. ko da yake har yanzu kotun bata bayyana ranar da za a rataye fitaccen malamin ba. Kotu a jihar Kano da ke Najeriya, ta yankewa fitaccen malamin nan Abduljabbar Nasiru Kabara hukuncin kisa ta hanyar rataya, bayan samunsa da laifin tayar da zaune tsaye da kuma bata suna ga fiyayyen halitta (S.A.W) Daga nan kuma ya yanke wa wanda ake tuhuma hukunci kan tuhume-tuhumen da ake yi masa. An dai gurfanar da Kabara a gaban kotu kan lamarin da ya shafi kalaman batanci ga Manzon Allah (SAW), matakin da ke iya tada zaune tsaye. A watan Yulin 2021 ne gwamnatin jihar Kano ta gurfanar da shi. Abduljabbar dai ya bayyana gaban kotun cikin nutsuwar da ba’a taba gani ba tun bayan fara shari’ar, yana mai ban carbi tare da sauraron karar. Da aka tambaye shi ko yana da wani abu da zai fada wa kotun, Barista Aminu Ado Abubakar, wanda ya tsaya a matsayin lauyan wanda ake kara, ya roki kotun da ta yi wa wan...

Peter Obi Bazai Iya Lashe Zaben 2023 ba___Chewar Gwamnan Jihar Anambra

 Peter Obi ba zai iya lashe zaɓen 2023 ba, Cewar Gwamnan Anambra Soludo. Gwamnan jihar Anambra Chukwuma Soludo, ya bayyana cewa jam’iyyar Labour (LP) na Peter Obi ba za ta lashe zaben 2023 ba.”  Soludo ya bayyana hakan ne a ranar Litinin a wata kasida mai suna ‘Tarihi ya nuna kuma ba zan yi shiru ba (Sashe na 1).  Ya ce: “Bari ya bayyana sarai: Peter Obi ya san cewa ba zai iya ba kuma ba zai yi nasara ba. Ya san wasan da yake yi, shi ma ya sani, kuma ya san na sani.   “Wasan da yake bugawa shine  babban dalilin da yasa bai koma APGA ba. Gaskiyar mugunyar gaskiya (wasu kuma za su ce, Allah Ya kiyaye) ita ce, akwai mutane biyu jam'iyun da ke neman takarar shugaban ƙasa, Jam'iyyun sune kamaraka APC da PDP sauran wasan kwaikwayo ne mai ban sha'awa.” Gwamanan ya ƙara da cewa ya riga da ya faɗa masa ra’ayinsa, Lallai babu wata tafarki ingantacciya gare shi a kusa da mukamai biyu na farko, kuma idan ba a kula ba, ba zai ma kusanci matsayi na uku ba ko da a wurin ƙ...

Cikin Hotuna

Hotuna: Comrd Bashir Yau Bashowa Hotunan Yadda: Maigirma Gwamnan Jihar Katsina Alh Aminu Bello Masari, ya Jagoranchi taron masu ruwa da tsaki na Jam'iyyar APC, wanda  ya gudana yau Lahadi a dakin taro na gidan Gwamnati.